Gwamnatin Najeriya Ta Umarci Shugabannin Jami’o'i Da Su Bude Jami’o’i, Dalibai Su Koma Karatu Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kula da jami'o'i (NUC) ta umarci shugabannin jami'a da su gaggauta bude makarantu kana dalibai su koma karatu. Wannan na fitowa ne daga wata wasikar da ke dauke da sa hannun daraktan kudi na NUC, Sam Onazi a madadin babban sakataren hukumar, Farfesa Abubakar Rasheed. Jairdar Punch ta ce ta samu wasikar ne kai tsaye daga hukumar, inda aka umarci shuganannin jami'o'i da masu gudanar dasu da su koma bakin aiki. Mudai ba muda abun cewa kawai namu ido da kuma bin umurni, amma dai bani tunanin hakan zai kawo karshen rikicin ASUU da gwamnatin Tarayya. ~ Comr Abba Sani Pantami