ATIKU YA SAN HALACCI: SHAIDA DAGA BAKIN MALAM ALBANIY ZARIA

 B


abban Malamin Musulunci Marigayi Sheikh Albaniy Zaria yace Atiku Abubakar mutum ne wanda baya manta halacci, yana mutumta mutane, Malam yayi wannan maganar ne a cikin darasin Littafin Fiqhus-seerah

Malam Albaniy Zaria yana bada labarin zaman karatun jami'ah da yayi a garin Yola jihar Adamawa, a lokacin yana zuwa gurin wata tsohuwar mata da ta iya dafa abincin sayarwa na gargajiya yana sayan abinci a gurinta

Malam yace Atiku Abubakar bai yi wayo ba a duniya mahaifinsa ya rasu, haka ya fara tasowa maraya a gurin mahaifiyarsa, ita ma daga bisani ta rasu yana karami, to ashe wannan tsohuwar mata da Malam Albaniy Zaria yake sayan abinci a gurinta ta taba rike Atiku a garinsu bayan da 'yan uwansa na uba sukayi watsi da shi

Malam Albaniy Zaria yace wani lokaci anyi yajin aiki na Malaman jami'ah ya koma Zaria, bayan kammala yajin aiki ya dawo Yola ya tarar da tsohuwar matar nan a cikin wata sabuwar daula, ashe ta samu ganin Atiku ne lokacin da ya zama Mataimakin Shugaban Kasa ya canza mata rayuwa, ya gina mata gida na alfarma da mota mai tsada

Malam Albaniy yace a binciken da yayi ya gano cewa Atiku mutum ne wanda baya manta halacci, kuma mutum ne wanda yake mutumta mutane musamman wadanda suka taimakeshi, abubuwa na banza da ake fada akan Atiku ba haka bane

Don haka muna kira ga 'yan uwa talakawan Nigeria ku zo mu nunawa Atiku Abubakar halacci, mu hadu mu zabeshi domin ya maye mana gurbin Shugaba Muhammadu Buhari Maigaskiya, Insha Allahu ba zamuyi da na sanin zabar Atiku ba domin ya san halacci

Yaa Allah Ka bawa Atiku Abubakar nasaran zama shugaban Kasarmu Nigeria da alheri

Rubutawa: Datti Assalafy

Comments

Popular posts from this blog

Hajiya Farida Musa Jauro, Dawisun Mubi Commend Dr. Betta Edu's Selfless Leadership and Compassion

GOMBE STATE GOVERNMENT AWARDS CONTRACT FOR THE REMODELING OF İDİ SHOPPING COMPLEX

Hajiya Farida Musa Jauro's Selfless Contributions to Mubi South and Adamawa State