Babu ta yadda Jam'iyar PDP Zata Karbi Gwamnati Ajahar Gombe, Kawai Yaudarankansu Sukeyi - Hon. Khalil Ahmed Nafada

 Babu ta yadda Jam'iyar PDP Zata Karbi Gwamnati Ajahar Gombe, Kawai Yaudarankansu Sukeyi - Hon. Khalil Ahmed Nafada


Babu tayanda Jam'iyar Adawa ta PDP Zata Karbi Gwamnati Ajahar Gombe domin Al'ummar Jahar Gombe Suna tare da Maigirma Gomna Dari bisa Dari.

Duk Wanda Yasan Siyasa Kuma Zaiyiwa Kansa Adalci da Maigirma Gomna Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya (Dan Majen Gombe) to tabbas yasan cewa Gomnatinmu ta Jam'iyar APC tayi dukkanin abunda yadace Acikin Wa'adin mulkinsu na farko, domin kuwa Al'ummar Jahar Gombe Sungani akasa.

Duk Wani Abu Dazai kawo cigaba Ajahar Gombe Maigirma Gomna yasamar dashi Ajahar Gombe, Kama daga Kan Hanyoyi Inganta Harkokin Kasuwanci, Da tabbabtar da Zaman Lafiya Ajahar, Wanda duk Wanda yashigo Jahar Gombe yasancewa Kwalliya ta biya Kudin Sabulun Domin Kuwa Mutanen Jahar Gombe Basuyi Zaben Tumun dare ba.

Idon Zamu ajiye bambancin ra'ayi Muduba Makomar Jahar Gombe to tabbas Koda Yan Jam'iyar PDP bazasu Zabi Dan Takaran Gomna Ajam'iyar tasuba, domin Kuwa Sukansu sunsan cewa Baidace yajagoranci Al'umma ba.

Bawai Ina maganane Amatsayin Mai Bawa Gomna Shawaraba, Ayau Ina maganane Amatsayina na Cikakken Dan Jahar Gombe Kuma Mai Kishi da son Ganin Cigaban Jahar Gombe, abaya Kowa yasan yanda mukayita Gogormaya alokacin Zaben Dubu biyu da Sha Tara, Wanda alokacin Jinina naki Nace Sai Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya domin Natabbata Shine yadace da Jagorancin Jahar Gombe.

Wasu da dama alokacin Sungujeni, Wasuma Jisuke kamar nayi Ridda domin Naki Nayi Usman Bayero Alokacin Sabida Sanin Cewa Bashine Yadace da Jahar Gombe ba, Ankai ruwa rana sosai Amma cikin iKon Allah Ayanzu kowa yagane manufarmu nason Kawo Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya domin Kuwa Kolliya ta biya Kudin Sabulu.

Siyasa ta mutane ne kuma Jama'a Suke alkalanci akan lamari na Siyasa, don haka Al'ummar Jahar Gombe Kaso Saba'in cikin Dari Suna tare da Dan Majen Gombe, domin Kuwa Sungamsu cewa Shine Daya tilo Dazai cigaba da ciremusu kitse awuta, Kasancewarsa mutum Mai Kishi da kaunar Cigaban Jahar Gombe.

Bana taba tunani ko Wani fargaba akan Zaben Dubu biyu da Ashirin da Uku domin Kuwa IInuwa Ko Gezau, Kuma Zamu kawo Asiwaju Bola Ahmed Tinubu domin inganta Rayuwar Al'ummah Kasarnan.

Hon. Khalil Ahmed Nafada (Shugaban Kungiyar Inuwa Ko Gezau) Kuma Mai taimakawa Gomnan Na Musamman Kan Isarda Sako Ga Jama'a.

Comments

Popular posts from this blog

Hajiya Farida Musa Jauro, Dawisun Mubi Commend Dr. Betta Edu's Selfless Leadership and Compassion

GOMBE STATE GOVERNMENT AWARDS CONTRACT FOR THE REMODELING OF İDİ SHOPPING COMPLEX

Hajiya Farida Musa Jauro's Selfless Contributions to Mubi South and Adamawa State