Britaniya Zata Kashe Fam Biliyan 60 Domin Rage Radin Tsadar Makamashi.


Birtaniya za ta kashe fam biliyan 60 don rage radadin tsadar makamashi ga 'yan kasar

Gwamnatin Birtaniya ta sanar da cewa sabon shirin da ta bullo da shi don taimakawa gidajen jama’a da kuma kananan masana’antu wajen biyan rabin kudin wutar da su ke sha, saboda tsadar makamashin da kasar ke fama da shi, zai lakume tsabar kudi Fam biliyan 60 ko kuma Dala biliyan 68 a cikin watanni 6 masu zuwa.

Sabon ministan kudin kasar, Kwasi Kwarteng ya shaidawa taron majalisar dokoki yau juma’a, yayin da ya ke cewa, su na fatar ganin adadin kudin ya dan ragu nan gaba, saboda tattaunawar da su ke yi da 'yan kwangila nan gaba.

Sabuwar Firaministar Birtaniya, Liz Truss ta bayyana aniyar saukakawa jama’ar kasar tsadar rayuwar da su ke fama da ita.

Tsadar makamashi a sassan duniya ba kadai Birtaniya ba, na da nasaba da yakin Rasha a Ukraine wanda ya kai ga katse iskar gas din da kasar ke fitarwa Turai. 

Al'ummar Birtaniya dai na ganin matsananciyar tsadar rayuwar da basu taba gani ba cikin fiye da shekaru 70 da suka gabata, matakin da ke zuwa dai dai lokacin da darajar kudin kasar ke karyewa.

Karon farko a cikin shekaru 378, kudin Ingila na Fam ya fadi da kashi biyu a kasuwar musayar da ake tsakanin sa da dalar amurka, yayin da kasar ke fuskantar koma bayan tattalin arziki.

📷 - Lizz/twitter

Comments

Popular posts from this blog

Hajiya Farida Musa Jauro, Dawisun Mubi Commend Dr. Betta Edu's Selfless Leadership and Compassion

GOMBE STATE GOVERNMENT AWARDS CONTRACT FOR THE REMODELING OF Ä°DÄ° SHOPPING COMPLEX

Hajiya Farida Musa Jauro's Selfless Contributions to Mubi South and Adamawa State