Buhari ya bukacemu da mu cire mataimakin shugaban kasa Osinbajo dana Boss Mustapha daga yakin neman zaben Tinubu – APC mai mulki

Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Jam'iyyar APC mai mulki ya yi ƙarin haske kan dalilin da ya sa ba a saka sunan mataimakin shugaban ƙasar Farfesa Yemi Osinbajo ba cikin kwamitin yaƙin neman zaɓe na Asiwaju Bola Tinubu.

A yau ne dai aka fitar da sunayen mutum 422 waɗanda za su jagoranci yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a ƙarƙashin Jam'iyyar APC.

Ƙaramin Ministan Ƙwadago na Najeriya Festus Keyamo wanda shi ne kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen ya tabbatar da cewa Shugaba Buhari ne ya ce kada  a saka sunan Osinbajo da sakataren gwamnati Boss Mustapha saboda za su mayar da hankali ne kan gudanar da ayyukan gwamnati.

Keyamo ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar sakamakon ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan sunayen da aka fitar.

Ya ce Buhari, a matsayinsa na shugaban kwamitin, shi ya bada umarnin kada a saka Osinbajo da Mustapha.

Ya ce dama gwamnati da ta damu da talakawa ba za ta bari duk jami'an gwamnati su bar ayyukansu su tafi harkar siyasa ba.

Osinbajo dai na daga cikin waɗanda suka nemi tsayawa takarar shugabancin Najeriya a APC sai dai bai samu nasara ba.

Comments

Popular posts from this blog

Hajiya Farida Musa Jauro, Dawisun Mubi Commend Dr. Betta Edu's Selfless Leadership and Compassion

GOMBE STATE GOVERNMENT AWARDS CONTRACT FOR THE REMODELING OF İDİ SHOPPING COMPLEX

Hajiya Farida Musa Jauro's Selfless Contributions to Mubi South and Adamawa State