Dalilin Da Yasa Babu Sunan Osinbajo AKwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu - APC
Dalilin Da Babu Sunan Osinbajo A Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu —APC
Daga Ja'afar Muhammad Alkali (Ɗan Mainoma)
Jam’iyyar APC mai mulki a kasa ta yi karin haske kan dalilin da ya sa ba a saka sunan Mataimakin Shugaban Kasar Farfesa Yemi Osinbajo ba cikin kwamitin yakin neman zabe na Asiwaju Bola Tinubu.
A Yammacin ranar Juma’a ce dai aka fitar da sunayen mutum 422 wadanda za su jagoranci yakin neman zaben Shugaban Kasa a karkashin jam’iyyar APC.
Da yake bayyana dalali, Karamin Ministan Kwadago kuma Mai Magana da Yawun Kwamitin Yakin Neman Zaben, Festus Keyamo, ya tabbatar da cewa Shugaba Buhari ne ya ce kada a kuskura a saka sunan Osinbajo da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha saboda za su mayar da hankali ne kan gudanar da ayyukan gwamnati.
Mista Keyamo ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a wannan Asabar din sakamakon ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan sunayen da aka fitar.
Osinbajo dai na daga cikin wadanda suka nemi tsayawa takarar shugabancin Najeriya a APC sai dai bai samu nasara ba.
Comments
Post a Comment