Gwamna Nysom Wike Yana Fadane Akan Gaskiya da Adalci – Chief Sam Nkire

 Gwamna Nysom Wike Yana Fadane Akan Gaskiya da Adalci – Chief Sam Nkire


Cif Sam Nkire, jigo a jam’iyyar All Progressives Congress, a ranar Laraba ya bayyana yakin da gwamna Nyesom Wike ya yi da jam’iyyar Peoples Democratic Party, a matsayin abin da ya shafi kasa baki daya da kuma neman hadin kan kasar ne.

A cewarsa, rashin biyayyar da jam’iyyar PDP tayi na mika mulki bayan mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawar da ruhin hadin kai, adalci da daidaito a kasar.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Larabar da ta gabata, Nkire yace Gwamna Wike na bukatar yabo daga dukkan ‘yan Najeriya kan yaki da tafarkin adalci domin ci gaban kasa baki daya.

Yayi nuni da cewa jam’iyyar PDP ta mayar da shugabancin kasar nan zuwa Arewa bayan mulkin shugaba Buhari ya kai ga rashin mutunta kundin tsarin mulkin Nijeriya, da duk Wasu ‘ya’yan jam’iyyar PDP daga Kudu da kuma al’ummar Nijeriya baki daya.

Yaci gaba da cewa yakin da Gwamna Wike ya yi a jam’iyyar PDP abu ne mai kyau wanda duk dan Najeriya mai kishin kasa dolene ya yaba masa, koda akidarsa ta siyasa, addini, kabilanci ko ra’ayinsa yasha ban ban Dana Gomnan, yana mai cewa kamata yayi a kalli hakan a matsayin hanya daya tilo da ya kamata ‘yan Najeriya subi.  Domin Samun ingantacciyar dimokradiyya mai lafiya.


Comments

Popular posts from this blog

Hajiya Farida Musa Jauro, Dawisun Mubi Commend Dr. Betta Edu's Selfless Leadership and Compassion

GOMBE STATE GOVERNMENT AWARDS CONTRACT FOR THE REMODELING OF İDİ SHOPPING COMPLEX

Hajiya Farida Musa Jauro's Selfless Contributions to Mubi South and Adamawa State