JAM'IYAR NNPP TA KOKA KAN SHIRIN APC NAYIMATA MAGUDI AZABEN 2023..


 2023: NNPP ta koka kan shirin APC na tafka maguɗin zaɓe a Kano 

Jam’iyyar  NNPP, ta kwarmata zargin shirye-shiryen tauye ƴancin masu zaɓe a zaɓen 2023 a Jihar Kano.

NNPP ta yi zargin cewa ta bankaɗo shirin da APC ke yi na rage yawan mutanen da ke da katin zabe na dindindin, PVC, a jihar ta hanyar yaudararsu su ƙwace su daga hannun al'umma.

Zargin na kunshe ne a cikin wata sanarwar bayan taro da Garba Diso da Hamisu Ali suka sanyawa hannu kuma aka mika wa manema labarai a karshen taron karawa juna sani na jam’iyyar NNPP, na yan takarar sanata, majalisar wakilai, yan takarar majalisar jiha da shugabannin jam’iyyar da aka gudanar a ranar 15 ga watan Satumba a Dutse. Royal Hotel.

Jam’iyyar ta ce ta lura da takaicin yadda a karon farko a tarihin mulki a jihar, mai rike da madafun iko ya mayar da al’amuran gwamnati tamkar na iyali, kamar yadda ake gani a manufofin gwamnati da nade-naden mukamai.

Sanarwar, a kokarin neman mafita cikin gaggawa kan barazanar da ke tattare da tauye ƴancin masu zaɓe, ta yi kira ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, da ta gaggauta buga tare da manna sunayen duk waɗanda su ka yi katin zaɓe amma basu karɓa ba domin a wayar da kan masu hakki su zo su karɓa.

Haka zalika sanarwar ta yi zarge-zarge da dama kan abinda ta kira rashin yin mulkin adalci da kuma lalata jihar Kano.

Daga bisani me ta kuma yi wa ƴan kasuwar waya ta Beirut Road da gini ya rufto wa, da kuma na Kantin Kwari da ambaliyar ruwa ta shafa jaje.

Comments

Popular posts from this blog

Hajiya Farida Musa Jauro, Dawisun Mubi Commend Dr. Betta Edu's Selfless Leadership and Compassion

GOMBE STATE GOVERNMENT AWARDS CONTRACT FOR THE REMODELING OF İDİ SHOPPING COMPLEX

Hajiya Farida Musa Jauro's Selfless Contributions to Mubi South and Adamawa State