Kotu ta kori Bwacha daga takarar gwamnan Taraba a APC

 


ata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Jalingo ta kori Emmanuel Bwacha, a matsayin dan takarar jam'iyyar APC na jihar Taraba.

Alkalin kotun Mai shari'ah Simon Amobeda ya kuma umarci APC ta gudanar da wani sabon zabe cikin kwana 14.

Kotun ta umarci hukumar INEC ta daina kallon Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar APC kuma shi ma sanatan mai wakiltar Taraba ta Kudu ya daina gabatar da kansa a matsayin dan takarar na APC.

Hukuncin ya zo ne bayan wata kara da David Sabo Kente, daya daga cikin masu neman takarar gwamna a APC ya shigar inda ya kalubalanci jam'iyyar da cewa ba ta yi zaben fid da gwani a tsakanin masu neman takarar gwamnan Taraba ba.

Mai shari'ah Amobeda ya bayyana zargin sanar da sakamakon karya da ake zargin baturen zabe ya yi a filin jirgin saman Danbaba Suntai, kafin ficewa daga jihar, a matsayin wani abu da bai dace ba.

Lauyoyin jam'iyyar APC da dan takarar da kotu ta kora sun ce za su yi nazarin hukuncin kafin yanke shawara kan mataki na gaba da za su dauka.

Comments

Popular posts from this blog

Hajiya Farida Musa Jauro, Dawisun Mubi Commend Dr. Betta Edu's Selfless Leadership and Compassion

GOMBE STATE GOVERNMENT AWARDS CONTRACT FOR THE REMODELING OF İDİ SHOPPING COMPLEX

Hajiya Farida Musa Jauro's Selfless Contributions to Mubi South and Adamawa State