Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Batun Tsayar Da Dan Takarar Shugaban Kasar PDP Daga Kudu


Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Batun Tsayar Da Dan Takarar Shugaban Kasar PDP Daga Kudu

Kotun Koli ta yi watsi da karar da aka shigar na neman tilasta wa Jam’iyyar PDP ta tsayar da dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023 daga yankin Kudu maso Gabas.

A ranar Juma’a Mai Shari’a Adamu Jauro, da ya jagoranci zaman kotun ya yi wasti da karar, bisa hujjar cewa kotun ba za ta iya sauraron sa ba.

Daya daga cikin wadanda suka yi zawarcin takarar shugaban kasa a PDP kuma tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Abia, Cosmos Ndukwe, ne ya maka jam’iyyar a kotu.

Ya garzaya kotu ne yana mai bukatar ta tilasta wa jam’iyyar ta rika amfani da tsarin karba-karban shugabanci.

A karar da ya shigar, Ndukwe, ya nemi kotun umarci jam’iyyar umarnin fito da dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023 daga Kudu maso Gabas — yankin da ya fito.

Amma Mai Shari’a Jauro ya ce mai karar ba shi da hujja, saboda batun tsayar da dan takara al’amarin cikin gida ne da ya kebanci jam’iyyun siyasa.

Comments

Popular posts from this blog

Hajiya Farida Musa Jauro, Dawisun Mubi Commend Dr. Betta Edu's Selfless Leadership and Compassion

GOMBE STATE GOVERNMENT AWARDS CONTRACT FOR THE REMODELING OF İDİ SHOPPING COMPLEX

Fake Support Group Exposed: Betta Edu New Media Centre Disassociates Self from Blackmail Attempt