Yan Bindiga Sunkaiwa Tawagar Sanata Uba Sani Hari Ajahar Kaduna


 Ƴan Bindiga Sun Kai Wa Tawagar Sanata Uba Sani Hari A Kaduna

’Yan bindiga sun kai hari kan tawagar dan takarar gwamnan Jihar Kaduna na jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani a babbar hanyar Kaduna zuwa Kachia.

akilinmu ya ruwaito cewa, ’yan bindigar da suka yi awon gaba da wasu kusoshin jam’iyyar biyu sun kai wa tawagar hari ne a Tashar Icce daf da Kasuwar Magani da ke yankin Kujama a Karamar Hukumar Kajuru da Yammacin ranar Alhamis.

Rahotanni sun ce, harin ya auku ne yayin da tawagar dan takarar gwamnan ke dawowa daga garin Kafanchan bayan halartar wani taron Shugabannin Kiristoci a Kudancin Kaduna.

Wata majiya wadda ta tsallake rijiya da baya, ta bayyana lamarin a matsayin abin tashin hankali.

Majiyar ta ce akalla motoci biyar ’yan bindigar suka bude wa wuta, lamarin da ya sa wasu daga cikinsu suka jikkata.

Majiyar Focus News Hausa, Aminiya ta samu Labarin cewa, Sanata Uba Sani ba ya cikin tawagar yayin da lamarin ya faru, inda wakilinmu ya ruwaito cewa kai tsaye ya wuce Abuja daga Kafanchan.

Sai dai Shugaban Kwamitin yakin neman zabensa, Sani Maina da Ahmed Maiyaki, wani jigo na jam’iyyar da wasu kusoshin jam’iyyar na cikin ’yan tawagar da harin ya ritsa da su amma suka tsira babu ko kwarzane.

Daga cikin wadanda ’yan bindigar suka yi garkuwa da su akwai wani dan takarar kujerar Majalisar Dokoki na Kajuru, Mista Madaki da wani Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Kajuru, Ruben Waziri.

Ben Maigari, wani dan uwan Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar da aka yi garkuwa da shi ya ce kawo yanzu dai ’yan bindigar ba su tuntube su ba.

Aminiya ta samu cewa, harin ya ritsa da wasu motocin gida biyu wadanda ba su da alaka da tawagar, inda ake fargabar mutum biyu daga cikinsu sun riga gidan gaskiya yayin da kuma ’yan bindigar suka tisa keyar wasu cikin jeji.

Da aka nemi jin ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar DSP Mohammed Jalige, ya ce zai yi wa wakilinmu karin bayani dangane da faruwar lamarin, sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai waiwayi wakilin namu ba.

Comments

Popular posts from this blog

Hajiya Farida Musa Jauro, Dawisun Mubi Commend Dr. Betta Edu's Selfless Leadership and Compassion

GOMBE STATE GOVERNMENT AWARDS CONTRACT FOR THE REMODELING OF İDİ SHOPPING COMPLEX

Hajiya Farida Musa Jauro's Selfless Contributions to Mubi South and Adamawa State