ZAƁEN 2023: Gwamnonin Arewa Guda 3 Za Su Marawa Peter Obi Baya A Zaɓen 2023, Cewar Kayode Ajulo
Daga Comr Nura Siniya
Wani lauya ƙwararre akan kundin tsarin mulki mai suna Kayode Ajulo, yace gwamnoni uku daga yankin Arewa sun amince su goyi bayan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, LP, Peter Obi kafin zaɓen 2023.
Haka zalika, Kayode ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa NAN a Abuja a yau Juma’a, game da babban zaben 2023 kamar yadda jaridar “Daily Nigerian ta ruwaito.
Sai dai ya lura da cewa Obi ya yi sanyin jiki game da burinsa na takara saboda bai kai ga tuntuɓar masu ruwa da tsaki a fadin kasar nan ba.
“Har yanzu zan ce Peter Obi bai shirya zama shugaban kasa ba saboda bai shirya tsallakawa kogin Neja ba har ma da kogin Owena,” in ji Ajulo.
Ya ce gwamnoni uku sun ba da alamun cewa za su goyi bayan yunkurinsa na zama shugaban Najeriya a 2023. inda ya ce aƙwai bukatar a yi amfani da lokacin, wanda kafin a fara yakin neman zabe na haƙika ya isa yankin arewacin Kasar domin ƙara neman goyon bayan dattawan yankin Arewa.
“Ajulo ya ƙara da cewa yana sane da gwamnoni uku daga Arewa da suka ba da alamun goyon bayansa. inda ya buƙaci Peter Obi, ya kai ga kudancin Najeriya ya kai ga yankin Arewa duka yankunan guda biyu domin “sayar da kan sa ga mutanen arewa gudun kada su canza ra'ayi.
Jaridar Hasken Arewa
Comments
Post a Comment