Daga Mujaheed Umar D Giwa. Jagoran Mabiya Shi'a a Nijeriya wato Shaikh Ibraheem Zakzaky yayi gyara ga wayenda suke ganin cewa, dole sai sun bar ɗariƙa ne kafin su zama Shi'a. Shaikh ɗin ya ke cewa, Ba dole ne sai mutum ya bar Darika ba sannan ya zama Shi’a, ana iya hada duk biyun in'an so, saboda daya Mazhaba ce, dayan kuma matafiyar Irfani ko Tasawwuf ce, ba bukatar sai mutum ya bar Tijjaniyya (kafin ya zama Shi’a). Mazhabar Malikiyya ne mutum zai bari sannan ya zama (mai bin Mazahabar) Jafariyya (Shi’a), amma yana iya yin Tijjaniyya.” Shaikh Zakzaky ya kara da cewa: “Idan mutum Shi’a ne, zai iya yin Qadiriyya zai iya yin Tijjaniyya, kuma yana Shi’arsa. Amma Mazhaba akwai ta Jafariyya (ba zai yi Malikiyya ba). Yace “Akwai bangarorin karatu a addinin nan guda uku muhimmai; na daya muna ce masa Tauhidi, wanda yake magana kan abubuwan da ya zama dole mutum ya yi imani da su, duk abin da za ka yi I’itikadinsa a zuciya shi yake magana a kai. Wato yana magana dangane ...